(ABNA24.com) Shugaban hukumar tsaro na farin kaya na Iran a yankin na Sistan da Balochestan, ya kuma kara da cewa; An yi nasarar kashe shugaban kungiyar ta Ta Jaish ul-Adil,mai suna Elyas Narouyee a yayin taho mu gama da jami’an tsaro.
Shi dai Narouyee daya ne daga cikin wadanda su ka jagoranci kai hare-hare akan dakarun kare juyin musulunci a lokaci daban-daban, daga ciki hadda harin da ya yi sanadiyyar shahadar wasu dakarun kare juyin juya halin musulunci biyu a Nikshahr.
Majiyar ta kuma kara da cewa; A ranar 8 ga watan Febrairu da ya shude ma, an tarwatsa wata kungiyar ta ‘yan ta’adda a cikin yankin,tare da kama wasu biyu da kuma lalata wani bom mai nauyin kilogram 5 da aka dasa a bakin ofishin ‘yan sanda a Zahedan.
/129